Rahoton yace Yarinya daya a cikin 10 ake yi wa fyade a duniya. Kuma Rahoton yace kimanin Yara 95,000 aka kashe a shekara ta 2012 kawai, yawanci a kasashen Latin Amurka.
Rahoton yace yara kanana da dama ne a fadin duniya ke fuskantar gallazawa, yawanci tsakanin ‘Yan shekaru biyu zuwa 14.
Yara ‘yan tsakanin shekara 15 zuwa 19, sun fi fuskantar cin zarafi daga abokan zamansu maza ko dai kafin aure ko kuma bayan aure. Kuma wannan a cewar rahon ya fi faruwa a kasashen Afrika da suka hada da Zimbabwe da Uganda da Tanzania da Jamhuriyyar Congo.
Rahoton kuma yace Najeriya ce aka fi samun mutuwar yara kanana da ake kashewa da gangan, kamar yadda rahoton yace matsalar ta fi yawa a kasashen Latin Amurka.
Rahoton ya bayyana fargaba ga ci gaban rayuwar yara kanana saboda yawaitar cin zarafinsu da ake samu a duniya. ABNA